ABINDA BELI A KOTU KE NUFI
ABINDA BELI A KOTU KE NUFI
Daga:
Nurudeen Dauda
13/09/2024
nurudeendauda24@gmail.com
nurudeendauda24@yahoo.com
nurudeendauda.blogspot.com
Abin da ake nufi da "Beli" a mahangar Shari'ar Bature shine ƙa'dar da ake sawa kafin abar wanda ake "zargi" da aikata "laifi" a gaban Kotu yaje gida domin ya riƙa zuwa zaman Kotu daga gidansa a maimakon a tsare shi a gidan yari yana zaman jiran hukunci.
A lokuta da dama akan sanya "ƙa'dar kuɗi" to amma ba biyan "kuɗi" na zahiri ake nufi ba anan, abin da ake nufi shine wanda zai tsaya a madadin wani zai kawo shedar mallakar "kuɗin" da aka sa a matsayin "Beli" domin idan wanda ya tsayawa ya gudu to shikenan anci Kuɗinsa. Hikimar haka shine kada wanda ake zargi ya gujema hukunci; ana saka ƙa'dar kuɗi ne saboda duk wanda zai tsayawa wani zai tabbata ya sanshi kuma idan ya gudu tofa zaiyi asarar kuɗinsa kuma babu mai son yayi asara.
A wasu lokuta akan bukaci a kawo shedar mallakar gida ko tsayawar wani babban ma'aikacin gwamnati ko tsayawar wani babban ba sarake. Dukkannin waɗanda suka tsawa wani ko wasu to dole suje su nemo sa ko su a duk inda yake ko suke ko kuma su fiskanci fushin hukuma.
Abin da ake zargin 'Yan sanda na karba a caji ofis cin-hanci- ne ba Beli ba.
Allah ya bama 'Yan zanga-zanga mafita.