AN GINA TASHAR RUWAN BARO NE A 1911
AN GINA TASHAR RUWAN BARO NE A 1911
Daga:
Nurudeen Dauda
11/7/2023
nurudeendauda24@yahoo.com
nurudeendauda24@gmail.com
nurudeendauda.blogspot.com
Tashar ruwan Baro (Inland-Port) itace tashar ruwan cikin k'asa ta farko a Nigeria. Turawan mulkin mallakane suka jayyo ruwan teku zuwa tashar Baro dake k'aramar hukumar Agaie ta jahar Niger a shekarun Alif d'ari tara da sha d'aya (1911) saboda mahimmancin ta ga harkan sifiri daga manya-manyan tekunnan Nigeria dake Kudancin k'asa zuwa "Arewaci".
Mayan jiragen ruwa na iya zuwa gab'ar tekunnan Nigeria (Sea ports) dake Kudancin Nigeria daga ko ina a sassan duniya banda Arewaci saboda babbanci yanayi. Shekaru arba'in da tara kafin bamu milkin kai Turawan suka samar da tashar domin k'ananan jiragen ruwa su sami isowa zuwa Arewacin Nigeria don inganta sifiri a wancan lokaci.
Turawan mulkin kuma sun gina layin dogo (Rail-line) daga tashar ruwan Baro har zuwa tashar jirgin k'asa dake garin Minna ta jahar Niger. Anyi kimanin shekaru hamsin da tara (59years) ana cin moriyar wannan tashar. Watau shekaru arba'in da tara kafin mulkin kai da kuma shekaru goma bayan mulkin kai.
Tashar wanda ke k'ark'ashin kulawar gwmnatin tarayya ta sami rashin kulawa ne daga farkon shekarun Alif d'ari tara da saba'in (1970). Sabida watsi da tekun da gwamnati tayi har ya kai matsayin se an yashe (dredge) tekun kafin a cigaba da aiki da shi.
Munyi shuwagabanni kamar su Generals: Gowon, Murtala, Obasanjo, Shagari; Generals: Buhari, Babangida, da Chief Shonekan. To amma sai a lokacin gwamnatin General Abacha a k'ark'ashin hukumar tattara rarar manfetur (PTF) k'ark'ashin General Buhari aka sami yunkuri na yashe tekun a inda har a kayi zane watau (complex design) don yashe tekun amma hakan bai samu ba. Wannan aiki bai sami kulawaba lokacin General Abdulsalami da kuma dawowar Gen. Obasanjo.
Gwamnatin Umar Yar'adua da tazo a 2007 tazo da yunkurin hab'aka sifirin na ta shoshin tekunnan cikin k'asa (Inland-Ports) a ciki harda Tashar Baro. Bayan rasuwan Yar'adua a 2010 sai aikin yasha ruwa. Gwamnatin Buhari da tazo a 2015 ta kammala yashe tekun har zuwa Tashar Baro a 2019. Gwamnatin Buhari ta k'addamar da kammala yashe tekun a watan janerun 2019.
Wani babban abin takaici da ban haushi shi ne duk yayata aikin da akayi tayi kama daga yink'urin shugaba Yar'adua na 2007 zuwa yau a shema babu hanyar mota daga tashar ruwan Baro zuwa cikin garin Baro. Wannan shi ya sanya har yau babu jirgin da yazo Baro tun bayan kammala yashe tekun.
Duk da bayar da kwangilar hayar mota daga Agaie zuwa Kacha zuwa Baro har 'yanzu ba a gama aikin ba. A b'angare daya kuma sai ma a kwananan ne aka bada kwangilar gyaran layin dogo mai tsawon 200km daga tashar ruwan Baro zuwa garin Minna.
Ya Allah ka temaki k'asa ta!