HARAMTA BARAN AL-MAJIRAI A KANO
HARAMTA BARAN AL-MAJIRAI A KANO
By:
Nurudeen Dauda
March 7th, 2024
nurudeendauda24@yahoo.com
nurudeendauda24@gmail.com
nurudeendauda.blogspot.com
Asalin Al-Majiranci a kasar Hausa ko Arewa bai dogara akan "bara"ba to amma sai gashi abin takaici yanzu "bara" a cikin tsarin tafi karatun yawa. A fahimtana Idan anaso dukkan wani mataki akan harkan Al-Majirci yayi tasiri tofa sai akalla jahohi goma shabiyar cikin sha tara na Arewa sun dauki mataki na baidaya.
AL-MAJIRANCI A KASAR HAUSA:
Asalalin kalmar "Al-majiri" ba kalmar "Hausa" bace, ansamotane daga kalmar larabci mai suna Al-muhajirin wato wanda yayi kaura daga wani muhalli ko gari zuwa wani. Kalmar Al-majiri jam'inta shine Almajirai. Al-majirai sune wanda sukayi kaura daga wani gari zuwa wani domin karatun Al-kur'ani mai tsarki. Al-majirci a kasar Hausa, an faroshi ne tun kaka da kakanni shekaru daruruwa da suka gabata tun kafin zuwan turawa .
Al-majiranci ya samo asaline akasar Hausa a sakamakon imanin da Al'umar Hausawa na wancan zanamin na iyaye da kakanni sukayi da cewa: (1) "Yaro" bazai iya samun karatu ba a gaban iyayensa saboda gata da jindadi na zama gaban iyaye.
(2) Dalili na gaba kuma shine imanin da Al'umar Hausawa na wancan zamanin sukayi dacewa baza'a taba samun ilminin karatun Al-Kur'ani mai tsarki ba cikin sauki ba wato dole sai ansha wahala sosai.
(3) Dalili na uku da Al'umar Hausawa na wancan zamani suke badawa shine cewa akwai karancin masana ilmin Al-Kur'ani mai tsarki a garuruwa a wancan zamani.
Al-majirci ko kuma Karatun Allo na tsangaya yana da kyakkyawan tsari daga matakin farko har zuwa matakin karshe . Akwai matakai kamar haka:
(1) Kolo wato matakin naziri a tsarin nasara, (2) Titibiri wato matakin firamare ,(3) Gardi wato matakin sakandire, (4) Malam wato matakin digiri na farko, (5) Alaramma wato matakin digiri na biyu, (6) Gwani wato matakin digiri na uku, PhD, da Kuma (7) Gangaran wato matakin Farfesa.
Alarammomi a locacin da dukkaninsu manomane sabanin yanzu kuma ba zaune suke a birane ba suna zaune a idan gonakinsu suke sabanin yanzu. Alokacin da Almajirai da iyayen yara suke turawa gabas kokuma garuruwan da banasu ba zaka samu cewa dukkaninsu sukkan taimakama malamamsu wajen noma abinda zasuci sabanin yanzu.
Iyayen yara wanda mafi yawancinsu suma manomane sukan tallafawa malaman 'yayansu da hatsi a wancan lokacin sabanin yanzu. Idan kuma sunfidda zakkarsu ta noma sukan baiwa malaman 'yayansu a wancan lokacin.
Azamanin da ake bin wannan tsarin na yarda malaman Al-majirai suna kusa da gonakinsu sabanin yanzu wanda dadama daga cikinsu suna birane tsarin yana tafiya yarda ya kamata. Taimakawar da iyayen yara sukeyi ya sanya tsarin ya tsayu sosai ta yarda tsarin ya samar da masana Al-Kur'ani maitsarki da dama. Masana da dama sun baiyana cewa zuwa cirani birane wanda malaman tsangaya na wancan lokacin sukeyi bayan wucewar damina shi yakawo da lilin barin kusa da inda konakinsu suke domin dawowa birane.
A wancan lokacin idan malaman tsangaya sunzo cirani a manyan birananmu masu kudi na wancan zamani sukan sauke malaman da Al-Majiransu a zaurukan gidajensu dan neman albarka Al-Kur'ani mai tsarki. A lokacin zamansu mutane da dama sukan kawo musu sadakokin abinci da makamantasu.
Masana da dama sun baiyana dalilin da yasa malaman tsangaya suka dawo zama a birane sabanin zamanin da. Bayan da malam tsangaya suka fara zuwa cirani jimkadan sai 'yan kasuwa masu neman ciniki da mata masu neman haihuwa da mata wadanda basason amusu kishiya da mata masu neman mazajen aure da sauransu suka fara zuwa neman Addu'o'i wajen malaman tsangaya wanda suka zo cirani a birane tare da kawo musu abin sadaka. Wannan yasa malaman sukaga cewa abinda ake samu abirane lokacin cirani yafi abinda ake samu a gonakinsu, wannan shi yasa da dama daga cikinsu suka dawo birane sabanin yanda tsarin yake a baya.
Dalilai guda uku da suka gabata da al'umar Hausawa na wancan zamanin kebadawa idan a wancan zamanin hujjane a yanzu dukkanin su duk sun kau.
Na daya (1) Idan azamanin da babu masana ilmin Al-Kur'ani mai tsarki a mafi yawancin garuruwan mu wanda yana daya daga cikin dalilan da yasa a ke tura yara wasu garuruwa dan neman karatu tofa a halin yanzu gidan kowa da akwai masu ilmin Al-Kur'ani mai tsarki.
Dalili na biyu (2) da ake badawa shine na cewa dole ne sai dalibi ya wahala kafin ya sami ilimi. Hujjoji da dama sun nuna cewa anyima abin fahimtane a kaikaice. Kyakkyar fahimta a game da wahala wajen neman ilmin ba yana nufin zama cikin yunwa da fatara ba a ma'ana mafi kyau yana nufin wahalar tilawa na yau da gobene da kuma rashin samun i'sarshen barci saboda neman karatu ba zama cikin faraba da wahala.
Dalili na uku (3) da suke badawa shine jindadi da gata na zama gaban iyaye. Misalai da dama na zahiri sun nuna cewa yaro zai'iya samun ilmin mai yawa a gaban iyayensa batare da sai ya bar gida yaje nesa ba. Akwai dubbannan yaro da suka haddace Al-Kur'ani a gaban iyayensu batare da sun bar gida sunje nesa ba. Wadanan yaro kuma baya ga karatun Al-Kur'ani da sukeyi a gaban iyayensu suna zuwa makarantar Boko don samun ilmin sana'a.
Al-majircin yanzu da muke gani ya sabama Al-majirci na asali wanda aka sani na iyaye da kakanni. Azamin da tsarin yana dogarone da kansa amma a halin yanzu kuwa tsarin ya zama wata hanya wanda iyaye ke gujema nauyin da Allah ya daura musu.
Bugu da Kari kuma shine na yarda Iyaye mata suka mayarda yaransu abin gasa da alfahari harma da gorantawa juna idan yaransu sun dawo gida hutu sun kawo musu tsarabar Al-majirci na zannuwa da sauransu feye dana abokanan zamansu ko makotansu.
Tura yara Al-majirci ya zama wata hanya wanda iyayen wannan zamanin ke gujema nauyin da Allah ya daura musu. Iyaye da dama suna ganin cewa tura yaransu Al-majirci sauke nauyin da Allah ya daura musune na ilmantar dasu. To amma a' kokarin sauke wannan nauyi guda daya watau na ilmantarwa wanda dayane kawai daga cikin dinbin hakkoki da Allah ya daurawa iyaye sai ake kyale sauran hakkoki da dama. A'misali baya ga hakkin Ilmantarwa, akwai na ciyarwa, na bada wurin zama, na sutura, na lalurar rashi lafiya da sauransu.
Iyayen yara na wannan zamanin sukan tura yaransu karatu wurin malaman da suma suna zaune a birane a rakube a zaurukan gidaje mutane ba'a kusa da inda gonakinsu yakeba. Malaman tsangaya na yanzu basa noma kamar yarda na zamanin da sukeyi, kuma iyayen yara na wannan zamanin basa kawoma malaman yaransu gudun mawar abinci dakuma zakkarsu na noma kamar yarda yake a zamanin da.
Idan har iyayen yara baza su bar yaransu suyi karatu na jeka ka dawo a gabansu ba to hanya mafi dacewa shine yazama dole iyaye su dauki nauyin yaransu. Kamar yarda iyayen da yaransu ke karatu a gabansu ke biyan kudin makarartar yaransu daku dukkan nauyinsu to suma iyayen yaran dake tura su nesa dan neman karatu yazama dole hukuma tasa ido domin atabbatar dacewa kowane uba idan zai tura yaransa karatu yazama dole yarika biyan kudin makaranta, na abinci, na sabulu, na manshafawa, na magani, na sutura da sauran su a kowane wata.
Lokaci yayi daya zama dole Al'umar Hausawa su sake tsarin karatun Al-majirci wanda akeyi halin yanzu domin kawo gyara a cikinsa. Rashin adalcine ace dukwanda yanemi da akawo gyara acikin tsarin Al-majirci na wannan zamani sai ayimishi yarfe dacewa shi makiyin karatun Al-kur'ani mai tsarkine. Munyi imani da cewa karatun Al-kur'ani mai tsarki dole ga Al-umar musulmi kuma babu wanda ya'isa ya hana yinsa to ammafa yazama wajibi da'a kawo gyara acikin tsarin. Dole Al-umar Hausawa su fahimci cewa kasashe da dama na musulmai suna da hanyoyin koyar da yaransu karatun Al-Kur'ani mai tsarki ba tare da barace-barace ba.
Allah yama Najeriya albarka!