SANA'AR KAYAN GWARI DA DABBOBI A KUDU
SANA'AR KAYAN GWARI DA DABBOBI A KUDU
By:
Nurudeen Dauda
15 February, 2021
nurudeendauda24@yahoo.com
nurudeendauda24@gmail.com
nurudeendauda.blogspot.com
"SABO TURKEN WAWA"
Locaci yayi da 'Yan Arewa masu sana'ar kayan Gwari kamar su "Albasa", "Tumatur", "Atarugu", "tattasai" da sauransu a kudancin Nijeriya su fahimci cewa zamani yayi nisa abubuwa sun canza . Bugu da k'ari , yakamata su hankalta a game da wannan abu dake faruwa locaci bayan locaci na asarar rayuka da dukiya.
Dukda yake dokar k'asa ta bada damar zama ko ina. Kuma hak'in gwamnatine ta kare rayuka da dukiyan 'yan k'asa ko a ina. A ganina mafita anan shine yin karatun ta natsu domin had'a kai a k'ungiyance don neman a samar masu da kasuwar kayan Gwari a jihar Kaduna ko a Neja ko a Nassarawa ko a gefen garin Abuja don dawowa a rik'a biyosu ana siyan kayansu.
Suma 'Yan Arewa masu sana'ar dabbobi a kudancin Nijeriya ya kamata dasu had'a kansu a k'ungiyance don a sama masu kasuwar dabbobi watau "Kara" ko a Kaduna ko a Neja ko a Nassarawa ko a Abuja don suma a rik'a biyosu ana siyan kayansu.
Kamar 'yanda 'Yan Arewa ma zauna gida masu sana'ar sayar da Lemo, Ayaba, Agada, Abarba, da Kwakwa da kuma danginsu ke zuwa kudancin Nijeriya don saro kayayyakinsu don sayarwa, haka suma ya kamata da su dawo Arewa a rik'a biyosu a na siyan kayayyakinsu.
Ya kamata 'Yan kasuwar mu na Arewa dake kudancin Nijeriya su gane cewa ana buk'atan kayansu kullum rana don rayuwar yau da gobe, saboda haka duk indda suka koma dole a biyosu.Wanda keda abin da ake buk'ata don rayiwa shiya kamata a biyo.
Kamar yarda 'Yan kasuwan Arewa ke zuwa kurmi sarin Goro haka ya kamata suma 'Yan kasuwan kudu surik'a zuwa Arewa sarin kaya a maimakon a rik'a binsu da shi hargida.
Wannan sabon tsarin zai taimaki 'Yan kasuwarmu wajen tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu. Bugu da k'ari, tsarin zai taimaki tattalin arzikin Arewa wajen samar da kud'ad'en Haraji kamar yarda 'Yan kasuwarmu ke biya a kudancin Nijeriya. Harkar abincin siyarwa, sifiri ,Otel- Otel ko d'akunan haya zai hab'aka a Arewa saboda masu zuwa siyan kaya daga kudu.
Nijeriya ba itace k'asar da tafi ko wace k'asa a doniya yawan k'abilu ko addinai ba. K'asar Hindiya ta fimu yawan k'abilu da addinai ma babbanta. Akwai k'abilu sama da dubu. Babu k'asar da ta kai Hindiya mabiya addinai ma babbanta.
Ya kamata 'Yan Nijeriya Hausawa,Yarbawa , iyamurai da sauransu su fahimci cewa Allah ne ya had'amu zama a k'asa d'aya babu kuma wanda ya isa ya kori wani a Nijeriya.
Allah ya temaki k'asarmu Nijeriya!